3 Janairu 2024 - 15:07
Adadin Shahidan Waki'ar Ta'addanci A Kerman Ya Kai Sama Da Mutane 100.

Shahidai Sama Da 100 A Fashewar Bom Kan Hanyar Kerman Shahidai Gulzar

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku rahoto kan wakiar data faru a yau a birnin Kerman: Wannan rahoton yana dauke da bidiyon yanayin Lokacin farko na fashewar bom a kan hanyar Kerman Shahidai Gulzar wanda Wannan bidiyon yana iya tayar da hankali.

Yawan shahidai da wanda suka raunata a fashewar Kerman Yana Ƙara haihawa wanda a cikin wannan ta'addancin dai sama da mutane 50 ne suka yi shahada sannan wasu sama da 100 suka jikkata.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali kuma akwai yiwuwar adadin shahidai ya karu.

Rahotanni sun ce fashewar ta farko ta kasance a nisan mita 700 daga kabarin Shahid Suleimani sannan kuma fashewar ta biyu ta faru ne a nisan kilomita daya da kabarin kuma ta kasance wajen titin maziyarta da shingayen bincike.